logo

HAUSA

Kamfanonin hada-hadar hannayen jari na Afirka sun gana a Nairobi

2023-11-24 10:05:34 CMG Hausa

Wakilai daga kasuwannin hada-hadar hannayen jari na Afirka sun shirya wani taron yini biyu a Nairobi, babban birnin kasar Kenya jiya Alhamis, domin inganta kasuwanci tsakanin kamfanonin hada-hadar hannayen jari.

Taron na shekara-shekara karo na 26 na kungiyar masu hada-hadar hannayen jari ta Afirka, ya hallara masu hada-hadar musanyar kudaden ketare 25 daga sassa daban-daban na nahiyar, domin gaggauta dunkulewar kasuwannin hannayen jarin nahiyar wuri guda

A jawabinsa na bude taron, shugaban kasar Kenya William Ruto, ya bayyana cewa, kamfanonin hada-hadar hannayen jari a kasashen Afirka, za su samar da dimbin masu zuba jari a kasuwannin hannayen jarin nahiyar.

Ana sa ran a duk tsawon taron, mahalarta za su samar da ingantattun hanyoyin magance kalubalen da sassan zuba hannayen jari ke fuskanta, da samar da ingantaccen tsarin hada-hadar kudi na bai daya maras gurbata muhalli a nahiyar.

Shugaban rukunin masu hada-hadar canjin kudi a Najeriya, Oscar Onyema, ya bayyana cewa, hada-hadar hannayen jari a Afirka, za ta mayar da nahiyar zama wata kasuwar hada-hadar hannayen jari ta bai daya. (Ibrahim Yaya)