logo

HAUSA

Shugaban kasar Nijar Abdourahamne Tiani ya kai ziyarar aiki da abokantaka a kasashen Mali da Burkina Faso

2023-11-24 20:34:57 CMG Hausa

Shugaban mulkin rikon kwarya na kasar Nijar, Janar Abdourahamane Tiani ya kai wani rangadin aiki da zumunci a kasashen Mali da Burkina Faso, a ranar jiya Alhamis 23 ga watan Nuwamban shekarar 2023. Wannan ziyara ita ce ta farko ta shugaban ta kwamitin ceton kasa na CNSP, tun bayan juyin mulkin da ya hambarar da tsohon shugaban kasa Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023.

Daga birnin Yamai abokin aikin mu Mamane Ada ya aiko da wannan rahoto.

 

Daga masalin karfe goma na safe ne na ranar jiya, jirgin saman dake dauke da shugaba Abdouramane Tiani ya tashi daga filin jiragen sama na kasa da kasa na Diori Hamani zuwa kasar Mali, inda ya samu tarbo daga shugaban rikon kwarya na kasar Mali, Kanal ASSIMI Goita a filin jiragen sama na kasa da kasa na shugaba Modibo Keita dake birnin Bamako. Rangadin ya rataya kan tsarin aiki da abokantaka. A yayin wannan ziyara ta ‘yan sa’o’i biyu a birnin Bamako, shugabannin kasashen biyu sun maida hankali kan muhimman abubuwan da suka shafi karfafa huldar dangantakar abokantaka tsakanin kasashen biyu, da kuma duba makomar kasashen biyu a cikin kungiyar kasashen yankin Sahel ta AES. A yayin wannan ziyara, shugaba Tiana ya samu rikiyar manyan jami’an gwamnati da na CNSP. Bayan kammala rangadin kasar Mali, Shugaban Nijar da tawagarsa sun tashi zuwa kasar Burkina Faso, duk dai a ranar Alhamis 23 ga watan Nuwamban shekarar 2023, inda shugaban rikon kwaryar kasar Kaftin Ibrahim Traore ya kebe musu babban tarbo. Nan ma shugabannin biyu sun tattauna makomar dangantakarsu da kuma duba hanyoyin ci gaban kasashensu. Ita dai wannan ziyara ta shugaba Tiani a kasashen Mali da BurkinaFaso ta farko tun kama mulkinsa ta bayyana niyyar kasashen kungiyar AES na gudu tare da tsira tare, da maida kokarinsu wajen yaki da ta’addanci cikin hadin gwiwa, da kuma lalubo hanyoyin bunkasa ci gaban nasu.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI, daga Yamai a jamhuriyar Nijar.