logo

HAUSA

Sha’awar Krist Caldwell ga wasan Wushu

2023-11-23 20:32:11 CMG Hausa

Krist Caldwell, mai bayanin wasan Sanda ne a gasar Wushu ta kasa da kasa karo na 16, wadda ke gudana yanzu haka a birnin Fort Worth na jihar Texas dake kasar Amurka. Mutum ne da ya shafe sama da shekaru 20 yana harkokin da suka shafi wasan Wushu (Wato wasan fada irin na kasar Sin).

Mista Caldwell mai shekaru kimanin 40, masanin shari’a ne Ba’Amurke, wanda ke zaune a Plano, birnin dake da nisan kusan mil 50 daga Fort Worth. Yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya bayyana rayuwarsa a wasan Wushu.

A cewar sa "Mahaifiyar mu ta kan dauke mu ni sa dan uwa na duk ranar Lahadi zuwa dakin karatu bayan mun tashi daga coci. A nan ne kuma wata rana na ga wani littafi game da wasan fada irin na kasashen gabashin duniya. Littafin ya kunshi nau’o’in wasan na kasashen Japan, da Koriya, da Sin, kai har ma da na Thailand, da nau’in damben boxing na Amurka. Lokacin da na kai ga karanta babi game da nau’in wasan na kasar Sin, sai na gano cewa, nau’in wasan na Sin shi ne tushen wasan baki daya, wanda ya samo asali daga wuraren bauta na Shaolin dake Sin, wato daga nan ne sauran nau’o’in wasan suka samo asali!"

Mista Caldwell ya kara da cewa, "Tabbas wannan ya burge ni. Daga nan ne kuma na ci gaba da nazarin nau’o’in wasan Kung Fu, irin su wanda ake yi ta kwaikwayon damisa, da maciji, kai har da nau’in kwaikwayon mashayin barasa, wanda ya kunshi kwaikwayon fadan wanda ya sha barasa ya bugu. Wannan ya ja hankali na. Nan take na kamu da son wasan fada irin na Sin a lokacin ban wuce shekaru 13 kacal ba. Bayan shekaru sama da 20 ina gwada wasan fada na Sin, sai ya zama wasan da na fi sha’awa. A gani na wasan Kung Fu, yana da banbanci da wasan taekwondo ko na kareti, saboda duk wani motsi a wasan Kung Fu yana da suna na musamman, kamar dukan sanda irin na sarki biri, ko duka irin na takobin Janar Kwan, (Guan Yu, wani janar din soji ne da aka taba yi da can a kasar Sin). Amma sai mutum ya karanta tarihi kafin ya san wadannan abubuwa masu nasaba da al’adu na da can”.

A ganin Caldwell, gwada wasan Kung Fu ya kunshi koyon al’adu, da tarihin dake da nasaba da wasan fada irin na kasar Sin. Ya ce ya samu damar haduwa da mutane daga kasashen duniya daban daban, ta wannan wasa na fada mai asali daga Sin, kana ya fafata sau biyu a gasar Wushu ta kasa da kasa a Sin. Don haka yake alfahari da ziyartar birane kamar Shanghai, da Beijing, da Chengdu, da damar da ya samu ta ganin dabbar panda. A cewarsa "Wannan wata dama ce mai kayatarwa!".

Kaza lika, Caldwell ya lura da yadda wasan fada irin na Sin ya ba shi zarafin ziyarta, da fahimtar wuraren tarihi da dama dake kasar Sin, kamar “Fadar Sarakuna ta Forbidden City” dake birnin Beijing. A cewarsa, "Wadannan gine gine da suka kasance masu tarihin tsawon shekaru dubbai kuma har yanzu suke nan, abubuwa ne masu matukar birgewa. Na yi matukar sa’ar koyon wasan fada na Sin, wanda ya koyar da ni abubuwa game da al’adu, na kuma gode da hakan. A gani na a shekarun baya, ba a san wasan fada irin na Sin sosai a Amurka ba. Amma zuwa jarumai irin su Bruce Lee a shekarun 1970, ya sa an fara fahimtar wasan, sai kuma su Jackie Chan da Jet Li. A yanzu kowa ya san wasan fada irin na Sin".

Caldwell ya lura da yadda aka rikar shigar da wasannin fada na Sin cikin manyan fina finan Amurka, ciki har da irin su “Star Wars”. Ya ce “Idan ka kalli irin fasahohin fada da aka rika nunawa a fim din “Star Wars”, za ka ga duk nau’in Kung Fu ne masu kayatarwa".

Har ila yau, a ganin Caldwell, fasahohin wasannin fada na Sin na bazuwa sosai zuwa yammacin duniya, ba wai kawai ta hanyar nishadantarwa ba, har ma da fannonin kiwon lafiya da karfafa jiki. Yana kuma ganin wasannin masu asali daga Sin na da babbar kasuwa nan gaba a Amurka.

Bugu da kari, Caldwell na ganin kamar yadda a al’adance wasannin makiyaya na “cowboy” ke wakiltar Amurka, haka ma Kung Fu ko sauran nau’o’in wasan fada na Sin ke wakiltar Sin. A ganin sa “cowboy” da Kung Fu tamkar Yin da Yang ne.

Ya ce “Wasannin “cowboy” na nuna karfi, da kirki, da jarumta, yayin da Kung Fu ke nuni ga hakuri, da karfi da taimakawa mai rauni. Don haka a gani na “cowboy” na wakiltar yammacin duniya, yayin da Kung Fu ke wakiltar Gabashi, amma idan an hada su baki daya, suna zama tamkar Yin da Yang ne”.

Caldwell ya kuma bayyana farin ciki da zuwan gasar kasa da kasa ta Wushu karo na 16 ko WWC, inda ya ce ta wasannin fada ana kara gina al’ummun bai daya tsakanin kasashen duniya daban daban.

Ya ce "Suna iya kawo al’adun su na gabashi nan, muna iya raba al’adun mu na yammaci tare da su idan sun zo, wannan wani tsarin musaya ne mai kayatarwa".

Wannan ne karo na 2 da Amurka ke kara karbar bakuncin gasar ta WWC, bayan ta karbi bakuncin ta a Baltimore na jihar Maryland a karon farko a shekarar 1995.