logo

HAUSA

An samu jinkirin sakin mutanen aka yi garkuwa da su a Gaza da tsagaita wuta

2023-11-23 10:38:57 CMG Hausa

Mai ba da shawara kan harkokin tsaron Isra’ila ya sanar a yammacin jiya Laraba cewa, an dage yarjejeniyar sakin mutanen da aka yi garkuwa da su a zirin Gaza domin yin sulhu na wucin gadi har zuwa ranar Juma’a a kalla.

Gwamnatin firaministan Isra’ila Benjamin Natanyahu ta kada kuri’ar amincewa da yarjejeniyar da sanyin safiyar Laraba, sannan ta sanar da cewa, yarjejeniyar tsagaita wutar za ta fara aiki a ranar Alhamis.

A karkashin yarjejeniyar da aka cimma, za a sako a kalla Isra’ilawa 50 da aka yi garkuwa da su a matsayin sakin fursunonin Falasdinawa a kalla 150 da ke hannun Isra’ila, da kuma shigar da kayan agaji da ake matukar bukata a Gaza. 

Sai dai daraktan majalisar tsaron Isra’ila Tzachi Hanegbi ya fada a yammacin jiya Laraba cewa, sakin wadanda aka yi garkuwa da su zai gudana ne bisa yarjejeniyar farko da bangarorin suka kulla, ba kafin ranar Juma’a. (Yahaya)