MDD na shirin janye dakarun wanzar da zaman lafiya daga DRC
2023-11-23 11:12:18 CMG Hausa
Tawagogin hadin gwiwa na tsara ayyuka a jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, sun tsara shirin janye dakarun rundunar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake aiki a kasar.
Da yake tabbatar da hakan a jiya Laraba, mataimakin kakakin babban magatakardar MDD Farhan Haq, ya ce za a janye dakarun rundunar ta MONUSCO ne cikin rukunoni daban daban, da taimakon abokan hulda na cikin gida da wajen jamhuriyar dimokaradiyyar Congo.
Farhan Haq, ya ce bayan ficewar dakarun, MDD za ta ci gaba da tallafawa ayyukan raya kasa da gwamnati da jama’ar Congo ke yi, da nufin wanzar da nasarar tsarin gina zaman lafiya da tsaron kasar. (Saminu Alhassan)