logo

HAUSA

Lablack Mourad: Sin ta sami babban ci gaba a fannin fasahohin kwaikwayon tunanin bil adama

2023-11-23 13:46:13 CMG Hausa

Sanin kowa ne cewa, kasar Sin da kasar Aljeriya suna da dangantakar abokantaka mai zurfi, kasashen biyu sun dade suna mutunta juna da daukar juna daidai gwargwado, kuma suna nuna goyon baya ga juna. Kuma irin wannan dangantaka mai kyau ta sanya dalibai na Aljeriya da dama zuwa kasar Sin don yin karatu, kuma dalibi mai suna Lablack Mourad yana daya daga cikinsu, inda yanzu haka yake karatun digiri na uku a jami’ar koyon kimiyya da fasaha ta Dalian dake kasar Sin, a cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku labarin wannan dan kasar Aljeriya, mai suna Lablack Mourad.