logo

HAUSA

Wakilan majalissar kungiyar ECOWAS sun bukaci da a janye takunkumin da aka kakabawa jamhuriyyar Nijar

2023-11-23 09:50:28 CMG Hausa

Wakilan majalissun dokokin kasashen kungiyar Ecowas sun bukaci shugabannin kasashen yammacin Afrika da su duba yiwuwar dage takunkumin da suka sanyawa Jamhuriyyar Nijar biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.

Sun bukaci hakan ne ranar Laraba 22 ga wata, yayin bikin bude babban taronsu karo na biyu na 2023 a birnin Abuja. Sun ce babu wani tasiri na hakika da takunkumin ya haifar illa kara ta’azzara rayuwar kunchi a tsakanin al’umomin Nijar da Najeriya.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Mahalarta taron da suka fito daga kasashe membobin kungiyar ta Ecowas sun bayyana damuwarsu cewa illar da takunkumin ya haifar bai tsaya ga yankunan da suka hada iyaka da kasar ta Nijar ba kawai, ya kawo nakasu ga safarar kayayyaki daga jihar Sokoto ta arewacin Najeriya zuwa kasar Ghana, haka kuma ya haifar da makamancin wannan matsala wajen dakon kaya daga kasar Togo zuwa Najeriya da ma sauran sassan kasashen dake cikin kungiyar ta ECOWAS, kama daga yammaci zuwa arewaci.

Sanata Ali Ndume memba ne a cikin kungiyar ’yan majalissar kasashen Ecowas din ya ce, takunkumin ya kara sanya talakawa musamman ma talakawan dake zaune a jihohin dake da iyaka da kasar ta Nijar cikin matsala.

“Mun san cewa Nijar ta yi iyaka da kusan jihohi 9 dake Najeriya wanda suka hada da Borno, Yobe, Kano, Katsina, Sokoto, Zamfara da Kebbi, kuma tun lokacin da aka kulle iyakoki tare da sanyawa kasar ta Nijar takunkumi, talakawa musamman mata da kananan yara ne suka shiga halin kaka-ni-ka-yi, kuma har yau babu wani ci gaba da aka samu wajen warware matsalar.”

Ya yi kira ga shugabannin kasashen dake cikin kungiyar ta Ecowas da su zartar da shawarar da kwamitin na kungiyar ’yan majalissun ya gabatar masu wanda yake neman su cire wannan takunkumi, sannan kuma su ci gaba da bin hanyoyin diplomasiyya wajen warware rikicin siyasar kasar ta Nijar. (Garba Abdullahi Bagwai)