logo

HAUSA

An kaddamar da kwamatin jagorancin shirin samar da kwararru a Najeriya

2023-11-22 10:26:38 CMG Hausa

Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Kashim Shettima ya kaddamar da kwamatin masu ruwa da tsaki daga bangarorin gwamnati da na ’yan kasuwa da sauran kungiyoyin bada agaji na kasa da kasa domin tafiyar da shirin gwamnati na samar da kwararru a bangarori daban daban tare kuma da gina al’umma.

A lokacin da yake kaddamar da ’yan kwamitin a fadar shugaban kasa dake birnin Abuja, Sanata Kashim Shettima ya kalubalanci ’yan kwamitin da su yi kokari wajen magance tazarar da aka yi wa Najeriya a duniya ta fuskar wadatuwar kwararru a fannoni da dama, sannan kuma su taimaka wajen kawo karshen matsalar talauci a tsakanin ’yan kasa.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Daraktan bankin duniya a Najeriya Mr. Shub-ham Chaud-huri da shugaban gidauniyar Dangote Alhaji Aliko Dangote, da Mr. Tony Elumelu jagoran gidauniyar Tony Elumelu Foundation da kuma ministan lafiya na tarayyar Najeriya Dr Ali Pate na daga cikin ’yan kwamitin.

Bayan kammala taron Ministan lafiya Dr Ali Pate ya shaidawa manema labarai cewa, “Gwamnati na duba hanyoyin da za ta bi wajen samar da yanayi mai kyau ta yadda za ta hada kai da kamfanoni domin dai ci gaban kasa.”

Alhaji Aliko Dangote a matsayinsa na daya daga cikin attajiran da za su kula da nasarar shirin ya yi alkawarin cewa, “Mu a matsayinmu na ’yan kasuwa masu bada gudummawa shi ne mu hada hannu da gwamnati domin dai tabbatar da ganin ta yi abun da ya dace, sannan kuma a shirye muke mu bada kudadenmu.” (Garba Abdullahi Bagwai)