logo

HAUSA

BRICS ta bi sahun sassan dake neman kawo karshen rikicin Isra’ila da Palasdinu

2023-11-22 17:20:00 CMG Hausa

Da yammacin jiya ne shugabannin kungiyar BRICS suka kira taron musamman kan batun Palasdinu da Isra’ila. Wannan ganawa na zuwa ne bayan wani muhimmin taron ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da na musulmi da kasar Sin ta jagoranta da nufin kawo karshen rikicin Israila da Palasdinu, ta yadda daga karshe za a kai ga tabbatar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

A jawabin da ya gabatar yayin taron shugabannin na BRICS ta kafar bidiyo daga birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, bisa la’akari da yanayin da ake ciki, ya zama wajibi kasashen BRICS su nemi a tabbatar da adalci da zaman lafiya kan batun Palasdinu da Isra’ila.

Abu mafi dacewa na kawo karshen rikicin da yaki-ci-yaki-cinyewa tsakanin Palasdinu da Isra’ila shi ne, aiwatar da shirin nan na “kafa kasashe biyu masu ’yancin cin gashin kai”, da dawo da halaltattun hakkokin Palasdinu da kafa kasar Palasdinu mai cin gashin kanta.

Shugaba Xi ya ce, idan har ba a warware matsalar bisa adalci ba, to, ba za a taba samun zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a yankin Gabas ta Tsakiya ba.

Galibin shugabannin kungiyar da suka yi jawabi, sun bayyana bukatar mutunta yarjejeniyar tsagaida bude wuta da sassan biyu suka cimma, wadda za ta kai ga sakin wadanda sassan biyu ke rike da su.

Kan haka shugaba Xi ya gabatar da shawarwari 3, inda ya yi kira da a dakatar da bude wuta domin cimma zaman lafiya da tsaro mai dorewa. Kuma dukkan bangarori masu rikici su dakatar da bude wuta da duk wani nau’i na rikici da kai hari kan fararen hula, a saki fararen hular da ake tsare da su domin kaucewa karuwar asarar rayuka da wahalhalu, a tabbatar da isar da kayayyakin agaji ba tare da tangarda ba da fadada ayyukan agajin jin kai ga mutanen Gaza da dakatar da tilasta musu kaura da katse wuta da ruwa da mai da ake wa al’ummar Gaza a matsayin hukunci na gama gari.

Masana na kira ga kasashen duniya da su dauki kwararan matakai domin kaucewa tsanantar rikicin da bazuwar tasirinsa kan baki dayan yankin Gabas ta Tsakiya. Baya ga wadannan muhimman taruka, shi ma babban sakataren MDD Anthony Guterres, ya bukaci da a kai zuciya nesa a mutunta dokoki da ka’idojin jin kai da bukatar kare rayukan fararen hula da kaucewa tsanantar rikici, ta yadda za a kai ga tabbatar da zaman lafiya a yankin baki daya. Wannan ya kara nuna muhimmancin wanzar da zaman lafiya a duniya maimakon yin fito na fito. (Ibrahim Yaya)