Wasu ’yan bindiga sun hallaka a kalla fararen hula 9 a wata kasuwa dake Kamaru
2023-11-22 10:40:18 CMG Hausa
Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan aware ne, sun hallaka a kalla fararen hula 9 tare da jikkata wasu sojoji 2, yayin wani harin da suka kaddamar a wata kasuwa mai yawan jama’a, dake yankin yammacin kasar Kamaru.
Da yake tabbatar da aukuwar harin, babban jami’in rundunar tsaron yankin Bamboutos, mista David Dalor Dibango, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewa, ’yan bindigar sun bude wuta kan al’ummun dake kasuwar kauyen Bamenyam, a yankin Ngalim ne da misalin karfe 7 na safiyar jiya Talata, lamarin da ya haifar da jikkatar fararen hula masu yawa, kana sun kone gidaje da dama yayin harin.
Dibango ya ce sun ziyarci wurin da lamarin ya auku, sun kuma ganewa idanunsu mummunar barnar da ’yan bindigar suka aikata. Kazalika sun bukaci al’ummun wurin da su kwantar da hankulan su, domin suna ci gaba da bincike da nufin cafke wadanda suka aikata wannan mummunar ta’asa.
Kauyen Bamenyam na da iyaka da yankunan arewa maso yamma da arewa maso gabashin Kamaru, yankunan da ake amfani da Turancin Ingilishi, kuma tungar ’yan aware mai fama da tashe-tashen hankula. Hukumomin tsaron na cewa, sau da dama ’yan awaren kan tsallaka iyaka zuwa yankin Ngalim domin kaddamar da hare-hare kan fararen hula da sojoji.
A tsawon shekaru 6 da suka gabata, ’yan awaren yankin na ci gaba da tada hankulan al’ummun yankunan biyu masu amfani da Turancin Ingilishi, suna masu ikirarin yunkurin kafa kasa mai cin gashin kai. (Saminu Alhassan)