logo

HAUSA

Yadda ganawar tawagar kasashen Larabawa da ta musulmi kan batun Palasdinu da Isra’ila zai kawo zaman lafiya a yankin

2023-11-22 09:55:40 CMG Hausa

Yanzu haka tawagar ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da na musulmi na ziyara a kasar Sin tun daga ranar 20 zuwa 21 ga wata.

Tawagar dai ta kunshi ministan harkokin wajen Saudiyya da mataimakin firaministan Jordan, kuma ministan harkokin wajen kasar da takwaransa na Masar da kuma ministar harkokin wajen kasar Indonesia. Sauran sun hada da ministan harkokin wajen Palasdinu da sakatare-janar na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa (OIC).

Yayin ziyarar, bangaren Sin zai yi tattaunawa mai zurfi tare da hada hannu da tawagar ministocin harkokin waje na kasashen na Larabawa da na musulmi, wajen ganin an yayyafawa rikicin Palasdinu da Isra’ila ruwan sanyi tare da kare fararen hula da warware matsalar ta hanyar da ta dace.

A tattaunawarsa da tawagar, minsitan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana cewa, Sin ta kiyaye tabbatar da moriyar kasashen Labarawa da na Musulmi, da nuna goyon baya ga Palasdinawa da su samu hakkinsu bisa doka. Kasar Sin tana goyon bayan kasashen Larabawa da na musulmi da su yi kokari kan wannan batu ta hanyar diplomasiyya. Ya kuma gabatar da ra’ayin Sin kan yadda za a daidaita rikicin zirin Gaza da batun Palesdinu, wato a aiwatar da kudurorin kwamitin sulhu na MDD da babban taron MDD, da tsagaita bude wuta nan da nan, da bin dokokin kasa da kasa, musamman dokokin jin kai na duniya.

Ya ce, tilas ne a saurari ra’ayoyin Palasdinawa game da makomar Palasdinu, kana ya kamata a yi la’akari da damuwar kasashen dake yankin. A tsara duk hanyoyin daidaita batun bisa shirin daidaita matsaloli tsakanin Palesdinu da Isra’ila, da kuma tabbatar da zaman lafiya da na karko a yankin. Masu fashin baki na da imanin cewa, aiwatar da manufar kafa kasashe biyu ne kadai mafita ga rikicin dake faruwa tsakanin sassan biyu. (Saminu, Ibrahim, Sanusi Chen)