logo

HAUSA

Majalissar dokokin kasar Afirka ta kudu ta kada kuri’ar rufe ofishin jakadancin Isra’ila dake Pretoria

2023-11-22 10:38:52 CMG Hausa

’Yan majalissar dokokin kasar Afirka ta kudu sun kada kuri’un amincewa da rufe ofishin jakadancin Isra’ila dake birnin Pretoria, tare da dage duk wasu huldodin diflomasiyya da Isra’ila, har sai ta amince da tsagaita wuta a zirin Gaza.

Yayin kada kuri’un, jimillar ’yan majalisun wakilan kasar 248, sun jefa kuri’un amincewa da kudurin, yayin da 91 suka jefa kuri’un kin amincewa. 

Jam’iyyar adawa ta EFF ce ta gabatar da kudurin, wanda kuma ya samu gobon bayan jam’iyyar ANC mai mulki. Majalissar dokokin dai ta ce ta dauki wannan mataki ne har sai Isra’ila ta amince da tsagaita bude wuta, tare da shiga shawarwarin da MDD ke shiga tsakani. (Saminu Alhassan)