Isra’ila da Hamas sun cimma matsayar musayar fursinoni
2023-11-22 15:27:12 CMG Hausa
A yau Laraba ne tsagin gwamnatin Isra’ila da na dakarun kungiyar Hamas suka tabbatar da amincewa da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza. Wata sanarwar da ta fito daga ofishin firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ta ce karkashin yarjejeniyar, Hamas za ta saki Isra’ilawa da take tsare da su, yayin da ita ma Isra’ilan za ta saki Falasdinawa dake hannunta, kana za ta bari a shigar da karin tallafin jin kai yankunan da ta yiwa kawanya.
Sanarwar ta ce bisa tanadin sakin fursunonin, Hamas za ta saki a kalla Isra’ilawa 50, mafi yawansu yara da mata, yayin da ita kuma Isra’ila za ta sako kimanin mata da yara kanana Falasdinawa 150 da take tsare da su a gidajen yarinta.
An tsara sakin mutanen ne a kananan rukunoni cikin tsawon kwanaki 4, za kuma a tabbatar da tsagaida wuta a duk tsawon kwanakin. Har yanzu kuma Isra’ila na matsa lambar a saki karin yara ’yan kasarta da ake tsare da su. Ta kuma gabatar da bukatar tsawaita wa’adin tsagaita wuta na kwana guda, ga duk fursunoni ’yan kasar ta 10 da Hamas ta amince za ta saka.
A nata bangare kuwa, kungiyar Hamas ta tabbatar da amincewa da wa’adin kwanaki 4 na tsagaita wuta, wanda aka cimma bisa shiga tsakanin kasashen Qatar da Masar, bayan shafe kwanaki 46 ana kazamin fada a yankunan bakin ruwa da Isra’ila ta mamaye. (Saminu Alhassan)