logo

HAUSA

Isra'ila ta amince da yarjejeniyar sakin wadanda aka yi garkuwa da su a Gaza tare da tsagaita bude wuta

2023-11-22 10:06:45 CMG Hausa

Mahukuntan Isra'ila sun amince da shawarar da kasar Qatar mai shiga tsakani a rikicin Isra’ila da Palasdinawa ta gabatar, na tsagaita bude wuta a Gaza, tare da sakin fursunonin Palasdinu, da shigar da karin agajin jin kai zuwa yankin da aka yiwa kawanya, yayin da ita kuma kungiyar Hamas, za ta sako mutanen da mayakanta suka yi garkuwa da su.

A wani labarin kuma, ofishin watsa labarai na gwamnatin Gaza na cewa, adadin wadanda suka mutu a zirin Gaza ya zarce dubu 14 tun bayan barkewar rikici tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas a ranar 7 ga watan Oktoba.

Babban daraktan ofishin yada labaran yankin Gaza, Ismail al-Thawabta ya bayyana a wani taron manema labarai cewa, daga cikin wadanda suka mutu, akwai yara 5,840 da mata 3,920, yayin da wasu fiye da dubu 33 suka jikkata.

Al-Thawabta ya bayyana cewa, adadin wadanda suka bace ya zarce 6,800 wadanda suka hada da yara da mata 4,500 da ake zaton suke binne a karkashin baraguzan gine-gine da hare-haren Isra’ila suka lalata.

Isra'ila dai na ta kai hare-hare a Gaza a makonnin da suka gabata, a wani mataki na mayar da martani kan harin ba-zata da kungiyar Hamas suka kai a kudancin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, inda mayakan Hamas suka kashe kimanin mutane 1,200 tare da yin garkuwa da sama da 200. (Ibrahim)