logo

HAUSA

Me Ya Sa Shirin Kasar Sin Dangane Da Batun Palasdinu Da Isra’ila Ya Samu Amincewar Duniya?

2023-11-22 21:37:46 CMG Hausa

 

Dangane da jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a yayin taron musamman ta kafar bidiyo tsakanin shugabannin BRICS kan batun Palasdinu da Isra’ila a ranar 21 ga wata, jaridar Al Ahram ta kasar Masar ta ruwaito cewa, kasashen Larabawa da na Musulmi suna mayar da hankali kan yadda har kullum kasar Sin take yin adalci kan batun Palasdinu da Isra’ila, sun kuma yaba mata sosai. Ana fatan kasar Sin za ta kara taka rawa kan batun.

Palasdinu da Isra’ila sun dauki wata guda ko fiye da haka suna bude wuta tsakaninsu a wannan karo, inda mutanen kasashen 2 fiye da 15500 suka rasa rayukansu, ciki had da kananan yara fiye da 5800 a zirin Gaza. A wannan yanayi ne a cikin jawabinsa a yayin taron musamman, shugaba Xi ya yi kira ga bangarori masu rikicin su dakatar da tsagaita bude wuta a tsakaninsu nan take, a tabbatar da wucewar kayayyakin agajin jin kai ba tare da tangarda ba, a yi kokarin kaucewa tsanantar rikicin da bazuwar tasirinsa a sauran sassan duniya. Ya kuma jaddada cewa, babbar hanyar kawo karshen rikicin da yaki-ci-yaki-cinyewa tsakanin Palasdinu da Isra’ila ita ce kafa kasashe biyu. Matakai 3 da shugaba Xi ya gabatar, matakai ne da wajibi ne a dauka yanzu da kuma a dogon lokaci, wadanda suka nuna manufar daidaita batun na Palasdinu da Isra’ila yadda ya kamata.

Me ya sa shirin kasar Sin ya samu amincewar Palasdinu da Isra’ila da ma sauran kasashen duniya? Saboda jama’ar Sin na rungumar zaman lafiya da adawa tashin hankali. Har kullum suna bayyana ra’ayoyi da tafiyar da harkoki bisa adalci. Sabanin yadda Amurka take mara wa Isra’ila baya, kasar Sin ba ta nuna son kai kan batun na Palasdinu da Isra’ila, tana yin adalci tsakanin bangarorin 2. Ta yi matukar fatan za a dakatar da bude wuta a tsakanin Palasdinu da Isra’ila, su yi zaman tare cikin lumana. Har kullum kasar Sin na rungumar gaskiya da adalci.(Tasallah Yuan)