logo

HAUSA

Guterres ya yi kira da a yi amfani da matakan da shugabannin duniya suka dauka don magance sauyin yanayi

2023-11-21 11:11:06 CMG Hausa

Magatakardan MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a yi amfani da matakan da shugabannin kasashen duniya suka dauka don magance matsalar sauyin yanayi.

Jami’in na MDD ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da rahoto game da gibin hayakin da ake fitarwa na shekarar 2023 na shirin muhalli na MDD, yana mai cewa, yanayin da ake ciki yanzu, yana kara jefa duniya cikin karuwar ma’aunin yanayi zuwa digiri uku.

Yana mai cewa, a takaice dai, rahoton ya nuna cewa, gibin hayakin da ake fitarwa, ya fi kama da kogon da ke cike da karya alkawura, da kashe rayuka, da kuma ruguza tarihi.

Ya ce, duk wadannan gazawar shugabanci ne, da cin amanar mutane masu rauni, kuma wata babbar dama ce da aka rasa. Don haka, wajibi ne shugabanni su daura damara a yanzu, su yi kokarin cika burika da ayyukansu, tare da ganin an kai ga rage hayakin da ake fitarwa.

Guterres ya ce, tsare-tsare na kasa na gaba game da yanayi, za su kasance masu muhimmanci. Saboda haka, dole ne a tallafa wa wadannan tsare-tsare da kudade, da fasaha, nuna goyon baya da hadin gwiwa, don ganin sun tabbata. Ya kara da cewa, nauyin dake wuyan shugabanni a taron MDD kan sauyin yanayi mai zuwa da zai gudana a hadaddiyar daular Larabawa (COP28) shi ne ganin hakan ya tabbata. (Ibrahim)