Kimanin yaran Nijeriya miliyan 100 ne ke fuskantar mummunan tasirin sauyin yanayi
2023-11-21 21:31:49 CMG Hausa
Asusun kula da kananan yara na MDD (UNICEF), ya yi kiyasin akalla yara masu rauni miliyan 100 ne mummunan tasirin sauyin yanayi ya shafa a Nijeriya, kasa mafi yawan al’umma a nahiyar Afrika.
Babbar jami’ar ayyuka ta asusun UNICEF a jihar Kano dake arewa maso yammacin Nijeriya, Farah Mahmud ce ta bayyana haka ga manema labarai jiya, inda ta ce Nijeriya ce kasa ta biyu mafi rauni a duniya ta fuskar yadda yara ke fuskantar tasirin sauyin yanayi. Tana mai cewa, kimanin yara miliyan 100 ne ke fuskantar matsalar tsanantar yanayi.
A don haka, ta ce asusun ya tsara wani shiri da zai wakana daga shekarar 2023 zuwa ta 2027, domin magance wasu batutuwan sauyin yanayi da raunin yaran, ta hanyar sanya shirin yaki da sauyin yanayi cikin dukkan bangarorin shirye-shiryensa. A cewarta, aiwatar da shirye-shiryen yadda ya kamata a Nijeriya, za ta samar da juriya kan matsalar sauyin yanayi. (Fa’iza Mustapha)