logo

HAUSA

Kamfanin RIIFO na kasar Sin zai kaddamar da katafaren kamfanin samar da bututan roba a Habasha

2023-11-21 10:32:38 CMG Hausa

Babban kamfanin samar da bututan roba na kasar Sin RIIFO, ya bayyana shirinsa na shiga kasuwar kasar Habasha, inda a jiya Litinin ya sanar da shirin kaddamar da katafaren kamfanin kayan bututan hada ruwa a yankin masana’antu na birnin Adama, fadar mulkin jihar Oromia.

Kamfanin RIIFO wanda ke hadin gwiwa da kamfanin cinikayya da zuba jari na EZM dake kasar ta Habasha, ya ce sabon kamfanin zai lashe kudi har dalar Amurka miliya 14.5.

Da yake tsokaci game da hakan yayin taron manema labarai a jiya Litinin, babban shugaban kamfanin EZM Esmelalem Zewde, ya ce manufar wannan muhimmin hadin gwiwa shi ne sauya tsarin samar da bututan roba masu nagarta da kare muhalli, wanda hakan zai taimaka wajen samar da ruwa mai tsafta, da inganta ayyukan gine-gine a Habasha.

Mista Zewde ya kara da cewa, sabon kamfanin da za a kaddamar cikin makon nan da sunan RIIFO, zai fara sarrafa nau’o’in bututan roba samfurin PPR, da HDPE, da PVC na aikin wayoyin lantarki, tare da dukkanin sassan hada su. (Saminu Alhassan)