logo

HAUSA

Guterres ya jinjinawa Sin game da shirya muhawara kan tasirin samar da ci gaba mai dorewa

2023-11-21 14:43:49 CMG Hausa

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya jaddada muhimmancin ingiza manufofin samar da ci gaban bil Adama, yana mai jinjinawa kasar Sin, bisa yadda ta shirya muhawara game da yayata zaman lafiya mai dorewa ta hanyar samar da ci gaba, a yayin taron kwamitin tsaro na MDD na jiya Litinin.

Mista Guterres ya ce, "Ci gaban bil Adama ne ke haska hanyar cimma nasara, da ingiza samar da kariya, da tsaro da zaman lafiya. Hakan ne kuma ya sa ingiza zaman lafiya, da zurfafa wanzar da ci gaba, da dunkule ci gaba suke tafiya kafada da kafada. Ina godiya ga gwamnatin kasar Sin, bisa kiran wannan zaman muhawara, wanda ke nuni ga alakar dake akwai tsakanin ci gaba da zaman lafiya mai dorewa”.

Kaza lika Guterres ya ce, ci gaba a matsayin sa shi kadai, ba zai iya wanzar da zaman lafiya ba, dole ne sai an hada da tafiya tare, da kuma tabbatar da dorewar ci gaban.  (Saminu Alhassan)