logo

HAUSA

Aikin samar da tsintsiyoyi

2023-11-21 20:44:59 CMG Hausa

Yadda ake sarrafa tsintsiyoyi bisa hanyar gargajiya ke nan a gundumar Laoting da ke lardin Hebei na kasar Sin, inda a cikin ‘yan shekarun baya aka yi ta bunkasa aikin samar da tsintsiyoyi a matsayin abun da zai taimaka ga kara kudin shigar manoman wurin. Alkaluman da aka samar sun shaida cewa, yanzu haka ana samar da tsintsiyoyi sama da miliyan 2.8 a kowace shekara, wadanda har ake sayar da su zuwa kasashen ketare da suka hada da Japan da Koriya ta kudu.