logo

HAUSA

Wasu sassan Najeriya na ci gaba da fama da cutar mashako

2023-11-21 09:41:54 CMG Hausa

Rahotanni daga Najeriya na cewa wasu yankunan kasar musamman na arewacin kasar na ci gaba da fama da bazuwar cutar mashako ta “diphtheria”.

Jihar Kano dake arewa maso yammacin kasar mai tarin jama’a, na cikin jihohin da cutar ke yiwa mummunar barazana, inda rahotanni ke cewa tana ta bazuwa zuwa sassan kananan hukumomin jihar.

A baya an yi tunanin cutar wadda wata nau’in baktiriya ke yadawa ta lafa, amma a baya bayan nan ta sake bullowa tare da bazuwa cikin sauri. Cutar “diphtheria” dai na shafar hanci, da makoshi, da fatar jiki a wasu lokuta.

Cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya ko NCDC a takaice, ta tabbatar da harbuwar sama da mutane 8,400 da cutar a Najeriya, kuma adadin masu dauke da cutar a jihar Kano kadai ya kai a kalla mutum 7,188, adadin da ya kai kaso 86 bisa dari na jimillar wadanda suka kamu da cutar.

Alkaluma sun nuna cewa, cutar “diphtheria” mai matukar hadari, ta bulla a akalla jihohi 19 cikin jimillar jihohin kasar 36, ciki har da birnin Abuja fadar mulkin kasar. Jihohin dake kan gaba wajen yawan bazuwar cutar sun hada da Yobe, da Katsina, da Borno, da Jigawa da Kaduna. (Saminu Alhassan)