Najeriya ta nemi hadin kan kasashen yammacin Afrika wajen dakile yaduwar kudaden haram a Nahiyar
2023-11-21 13:44:50 CMG Hausa
Najeriya ta yi kira ga cibiyar dake yaki da safarar kudaden haram a yammacin Afrika GIABA da ta samar da wani tsari da zai karfafa dokokin da suka jibinci hukunci ga masu aikata wannan laifi a nahiyar.
Ministan shari’a kuma babban Atoney Janaral na Najeriya Lateef Fagbemi ne ya yi kiran a birnin Abuja ranar litinin 20 ga wata yayin taro karo na 27 na kwamitin ministocin cibiyar wadda ke karkashin kungiyar Ecowas.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Ministan shari’ar na tarayyar Najeriya wanda shi ne shugaban kwamitin ministocin, ya bukaci gwamnatocin dake yammacin Afrika da su rinka fifita manufofinsu na yaki da hada-hadar kudaden haram da kuma sauran laifukan da suka shafi kudade.
Yin hakan, a cewarsa, zai baiwa cibiyoyin lura da harkokin kudaden na kasashen kwarin gwiwa wajen toshe duk wasu kafofi da suke baiwa masu aikata irin wannan laifuka dama.
Ya ce, ka’idojin hada-hadar kudade da ake kokarin tabbatar da ganin ana bin su sau da kafa, ba wai ana yi ba ne da nufin takurawa jama’a, sai dai kawai domin tabbatar da tsaro da mutuncin kasashe da al’ummar dake kasashen ta fuskar mu’amalla na gaskiya ba tare da cin amana ba.
Ministan ya kuma bukaci mahalarta taron cewa, “A matsayinmu da muke wakiltar kasashenmu, wajibi ne mu dauki wannan taro a matsayin tubali na zurfafa nazari sosai a kan al’amuran cikin gidan kasashenmu, kamar yadda nake da yakinin yi a Najeriya.”
A jawabinsa yayin taron, shugaban hukumar kungiyar Ecowas Dr. Omar Touray wanda kuma ya samu wakilcin Mr. Mambury Njie alkawari ya yi na cewa, zai marawa cibiyar yaki da safarar kudaden GIABA ta hanyar daukar matakai da za su kai ga karfafa ribar da take samu a wannan gwagwarmaya tare kuma da kira ga kasashe membobin kungiyar da su dauki matakai na zahiri da zai shawo kan banbance-banbancen da ake samu a tsakaninsu musamman ma ta fuskar karfafa gwiwar cibiyoyin dake kula da shige da ficen kudade da kuma hukumomin tsaro na kasa da kasa. (Garba Abdullahi Bagwai)