logo

HAUSA

An yi wata ganawa a birnin Yamai tsakanin faraministan gwamnatin rikon kwaryar Nijar da wakilin bankin duniya dake kasar

2023-11-21 16:58:12 CMG Hausa

A ranar jiya Litinin 20 ga watan Nuwamban shekarar 2023, an yi wata tattaunawa a karo na biyu tsakanin faraministan gwamnatin rikon kwaryar kasar Nijar da wakilin bankin duniya, wannan ganawa na cike da fatan alheri a idon yawancin al’ummar Nijar tun bayan zuwan sojoji kan karagar mulki da kusan fiye da watanni uku.

Daga birnin Yamai abokin aikinmu, Mamane Ada ya aiko mana wannan rahoto.

A wajen karfe uku na yamma ne, faraministan gwamnatin rikon kwaryar kasar Nijar, malam Ali Mahamane Lamine Zeine ya gana a fadarsa dake birnin Yamai, da babban wakilin musamman na bankin duniya dake zaune a birnin Yamai, mista Han Fraeters.

Sai dai ba abin da ya fito ko gabatar da wata sanarwa gaban ’yan jarida, bayan wannan ganawa ta ’yan sa’o’i tsakanin manyan jami’an biyu, in ji kamfanin dillancin labarai na kasar Nijar ANP.

A rike cewa, tun bayan juyin mulkin da ya hambarar da shugaba Mohamed Bazoum a ranar 26 watan Yulin shekarar 2023, bankin duniya dake zuba kudinta kan manyan abubuwan more rayuwar jama’a da dama a jamhuriyar Nijar ta dakatar da ayyukanta dake shafar fannoni daban daban a cikin wannan kasa da ke yammacin Afrika.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.