logo

HAUSA

Me Ziyarar Ministocin Wajen Kasashen Larabawa Da Musulmi A Kasar Sin Ke Nufi?

2023-11-21 16:37:33 CMG Hausa

A farkon wannan mako ne ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da na musulmi suka kawo ziyara kasar Sin domin tattaunawa da takwaransu na kasar Wang Yi, game da rikicin Palasdinu da Isra’ila.

To me ya sa a duk cikin kasashen duniya da ma kasashen dake kiran kansu manya, wadannan kasashen Larabawa da Musulmi suka zabi kasar Sin da ta zama kasa ta farko cikin kasashen da za su kai ziyara?

Da farko dai, ya nuna yadda kasashen duniya ke ganin kima da darajar kasar Sin. Kuma kowa ya san cewa, ba haka kawai ake samun wadannan abubuwa ba, suna samuwa ne idan mutum ko wata kasa ta nuna cewa ita din ta san ya kamata, kuma ba ta nuna son kai ko fifiko ko danniya. Wadannan, dabi’u ne da Sin ke adawa da su, a don haka take mayar da hankali tare da yin kira da a yi hulda bisa mutuntawa da girmama juna tare da kauracewa yin katsalandan cikin harkokin gidan kasashe.

Abu na biyu shi ne, wadannan kasashe sun kwana da sanin cewa, kasar Sin ba ta gindaya sharudda kafin ta bayar da taimako ko ta yi wani abu da zai amfanawa duniya. Burin kasar Sin har kullum shi ne, a gudu tare a tsira tare domin samun duniya mai zaman lafiya da ci gaba da kuma al’umma mai makoma ta bai daya.

Tun da dadewa kasar Sin ta yi ta bayyana cewa, hanya daya tilo ta warware rikicin Palasdinu da Isra’ila, shi ne aiwatar da kudurin majalisar dinkin duniya na kafa ’yantattun kasashe biyu. Tun farkon fara rikicin, a lokacin da kasashen dake kiran kansu manya suka fito daya bayan daya suna nuna bangaranci da rura wutar rikicin, kasar Sin ta yi abun da ya kamata babbar kasa ta yi, wato kira da a kai zuciya nesa ba tare da ta goyon bayan wani bangare ba. Shaidu sun riga sun tabbatar mana da cewa, ba kowacce matsala ba ce karfin soja ko yaki za ta iya warwarewa. Kamar yadda Sin din take kira a kullum, kwance damarar makamai da komawa teburin sulhu, su ne hanyoyi mafi dorewa na warware rikice-rikice cikin lumana. Don haka, ko shakka babu, wadannan kasashe na Larabawa, na da yakinin cewa, babu wata kasa da ta dace su yi shawarwari da ita don shawo kan matsalar kamar kasar Sin.

Shawarwari da manufofin da kasar Sin take gabatarwa a duniya sun nuna cewa, ita din ba ta kaunar rikici ko tashe-tashen hankula. Kuma wani kudurin MDD da aka kada a kwanakin baya da zummar tsaigata rikicin Palasdinu da Isra’ila, ya tabbatar mana da cewa, wannan ra’ayi na kasar Sin ya yi daidai da ra’ayin galibin kasahen duniya. (Fa’iza Mustapha)