logo

HAUSA

Kokarin Hadin Kai Don Samar Da Isasshen Abinci A Nahiyar Afirka

2023-11-20 22:00:21 CMG Hausa

A yau an kaddamar da taron kolin tabbatar da wadatar abinci a duniya a kasar Birtaniya don neman daidaita matsalar rashin isasshen abinci dake dada tsananta sakamakon sauyawar yanayi, da rikicin siyasa, gami da tafiyar hawainiyar tattalin arzikin duniya. Wani rahoton hukumar samar da abinci da raya aikin gona ta MDD ya nuna cewa, a halin yanzu, akwai mutane kimanin miliyan 735 dake fama da yunwa a duniyarmu, adadin da ya karu da miliyan 122 bisa na shekarar 2019. Kana a kasashen Afirka 35 dake kudu da hamadar Sahara, kimanin mutane miliyan 146 na fuskantar matsalar rashin isasshen abinci.

Ta yaya za mu iya daidaita wannan matsala? Daya daga cikin matakan da ake iya dauka, shi ne hadin kai tsakanin mabambantan kasashe ta fuskar kimiyya da fasaha masu alaka da aikin gona, don raya tsare-tsaren aikin gona masu inganci a duk fadin duniya. Kana kasar Sin da kasashen Afirka sun riga sun cimma dimbin nasarorin da za su iya zame wa sauran kasashe misalai a wannan fanni.

Yanzu a dimbin kasashen dake nahiyar Afirka, nau’in amfanin gona na kasar Sin, da fasahohin kasar a fannin aikin gona, sun sa ana samun girbi mai armashi, da kwantar da hankalin jama’ar kasashen Afirka a fannin wadatar abinci. Misali, a jihar Morogoro ta kasar Tanzania, wasu kwararru Sinawa daga jami’ar nazarin aikin gona ta kasar Sin sun yada fasaha mai inganci ta shuka masara, inda har yawan masarar da ake girbi ya ninka sau 3. Sa’an nan sun ci gaba da yada fasahar shuka wake tsakanin masara, don baiwa manoman wurin damar samun karin kudin shiga. Yanzu haka ruwan wake da Sinawa suka saba da shansa, wanda ake samu ta hanyar dafawa, da nikawa, da tace wake, ya zama wani nau’in abinci mai farin jini a jihar Morogoro ta kasar Tanzania. Kana wasu manoma sun samu karin kudi ta hanyar shuka wake, da sayar da ruwan wake, har ma sun bude wuraren cin abinci na kansu. Wato, ba kawai sun kawar da matsalar yunwa ba, har ma sun kama hanyar samun wadata.

Sai dai a fannin noman sauran amfanin gona, tabbatar da samun girbi mai armashi bai isa ba. Misali, rogon da ake yawan nomansa a kasashen Afrika. Idan an yi girbin rogo, dole ne a sarrafa shi cikin sa’o’i 48, don hana shi lalacewa. Wannan halayya ta kan sa a samu hasarar kashi 40% cikin rogon da aka girbe, a wasu kasashen dake nahiyar Afirka. Saboda haka fasaha mai inganci a fannin sarrafa rogo tana da muhimmanci sosai, abin da ya sa ta zama wani muhimmin bangaren da Sin da Afirka suke hadin kai a kansa. Yanzu haka, a cikin wata cibiyar nuna fasahohin aikin gona masu inganci da kasar Sin ta gina wa kasar Kongo Brazaville a matsayin tallafi, wasu injuna na sarrafa rogo na aiki cikin sauri, inda wadannan injuna ke wankewa, da yayankawa, da nikawa, da busar da rogo, da mai da shi gari. A cewar Paul Ngobo, minista mai kula da aikin gona, da kiwon dabbobi, da kamun kifi na kasar Kongo Brazaville, ta hanyar sarrafa rogo da injunan zamani, ana iya samar da garin rogo ga jama’a ta wani farashi mai karko, kuma an sa bukatarsa ta karu, baya ga taimakawa manoma samun karin kudin shiga.

Hakika, a yanzu haka, hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a fannin fasahohin aikin gona, bai tsaya a kasa ba, har ma yana wakana a sararin samaniya. Kasar Sin ta yi amfani da taurarin dan Adam wajen tsara fasahohin binciken yanayin aikin gona daga nesa, kana kasar ta koyar da fasahar ga duk kasar dake da bukata, ba tare da karbar kudi ba, don taimaka musu wajen binciken yanayin aikin gona, da samun alkaluman da ake bukata, ta yadda za a iya tsara ayyukan noma cikin kima, da tinkarar bala’i daga indallahi yadda ya kamata. Rakiya Abdullahi Babamaaj, mataimakiyar darektan sashen kula da tsare-tsare masu alaka da fasahohin sararin samaniya na hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Najeriya, ta taba halartar aikin da kasar Sin ta tsara a wannan fanni, gami da samun horo. Ta ce, nazarin hadin kai da ake yi, da ayyukan karfafa kwarewa, sun samar da fasahohi da bayanai da kasar Najeriya take bukata, a kokarin ta na cimma burin kawar da yunwa.

Akwai misalai masu tarin yawa, na hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka don tabbatar da samar da isasshen abinci ga al’ummun nahiyar Afirka. Sai dai me ya sa kasar Sin ke son zuba dimbin kudi don gudanar da hadin kai a wannan fanni? Dalili shi ne ra’ayin kasar Sin na samun “al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya a duniya”. Abin da ra’ayin ya kunsa ya shafi kula da bukatar sauran kasashe, yayin da ake neman biyan bukatun kai, da tabbatar da ganin ci gaban kasashe daban daban na bai daya, yayin da ake kokarin raya kai. A ganin kasar Sin, jama’ar duniya na da babbar moriya ta bai daya. Idan dimbin mutanen dake nahiyar Afirka na fama da yunwa, to, ba za su samu kudin sayen kayayyaki kirar kasar Sin ba. Kana idan tattalin arzikin kasashen Afirka ya kasa samun ci gaba, to, kamfanonin kasar Sin ma za su rasa damammaki na habaka zuba jari don samun karin riba. Wannan ra’ayi na tabbatar da moriyar juna, da moriyar bai daya, ya sa hadin gwiwar Sin da Afirka zai dore. Tun da ba mataki ne da aka dauka bisa tausayi ba, to, ba za a nuna girman kai, ko kuma tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe ba. Ta haka, hadin gwiwa zai iya haifar da karin nasarori, da sauye-sauyen yanayi mai armashi ga duniyarmu. (Bello Wang)