An fara yakin neman zabe a DRC
2023-11-20 10:26:08 CMG Hausa
An fara yakin neman zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki da na kananan hukumomi da aka shirya gudanarwa a ranar 20 ga watan Disamba shekarar 2023 a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo DRC.
‘Yan takara 26 ne za su fafata a zaben shugaban kasa da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (CENI) ta yi wa rajista, ciki har da shugaban kasar Felix Tshisekedi dake neman ya zarce.
A cikin wata sanarwar manema labarai da aka fitar a daren Asabar a birnin Kinshasa, shugaban CENI, Denis Kadima, ya yi kira ga ‘yan takara da su mutunta dokoki da kyawawan ka’idojin zabe a yakin neman zaben da zai dauki tsawon wata guda.
Shugaban kasar Felix Tshisekedi ya yanke shawarar kaddamar da yakin neman zabensa ne a jiya Lahadi a Kinshasa, babban birnin kasar DRC, inda dubban magoya bayansa suka taru a filin wasan shahidai na birnin.
Moise Katumbi, tsohon gwamnan lardin Katanga, wanda kuma shi ne shugaban kawancen ‘yan adawa kuma babban dan adawar Tshisekedi, ya zabi birnin Kisangani da ke arewa maso gabashin kasar, domin fara yakin neman zabensa a ranar Lahadin. (Yahaya)