logo

HAUSA

Yawan Falasdinawa da suka mutu a Gaza ya zarce 13000

2023-11-20 09:34:14 CMG Hausa

Ofishin yada labarai na gwamnatin zirin Gaza ya sanar a jiya Lahadi cewa, adadin mutanen da suka mutu a zirin ya zarce 13000 tun bayan barkewar rikicin Isra’ila da kungiyar Hamas a ranar 7 ga watan Oktoba.

Babban daraktan ofishin yada labarai Ismail al-Thawabta ya bayyana a wani taron manema labarai cewa, daga cikin wadanda suka mutu, akwai yara 5,500 da mata 3,500, yayin da wasu fiye da 30,000 suka samu raunuka daban-daban.

Al-Thawabta ya ce, adadin wadanda suka bace ya zarce 6,000 da suka hada da yara da mata 4,000 da har yanzu ke karkashin baraguzan gine-gine da hare-haren Isra’ila suka lalata.

Isra’ila dai ta ci gaba da kai hare-hare a Gaza a makonnin da suka gabata domin mayar da martani kan harin ba-zata da Hamas ta kai a kudancin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, inda mayakan Hamas suka kashe kimanin mutane 1,200 tare da yin garkuwa da sama da 200. (Yahaya)