Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sallami fursunoni 4,068 da suke tsare a sassan kasar daban daban
2023-11-20 09:56:58 CMG Hausa
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta salllami fursunoni 4,068 da suke a tsare, a wani mataki na rage cunkoso a gidajen gyaran hali dake sassan kasar daban daban.
A lokacin da yake kaddamar da tsarin sallamar fursunonin a gidan gyaran hali na Kuje a birnin Abuja, Ministan al’amuran cikin gida na tarayyar Najeriya Dr. Olubunmi Tunji-Ojo ya ce, sallamar ta biyo bayan kudin tarar da wasu attajirai da kungiyoyi suka yi ne ga daurarrun da suka gaza biyan tarar da kotu ta yi musu.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.####
Ministan ya ce, kafin sallamar wadannan fursunoni da aka yi a ranar 17 ga wat ana Nuwamba, adadin mutanen da suke tsare a gidajen gyaran hali 253 dake Najeriya ya kai dubu tamanin da dari takwas da hudu. Lamarin da ya haura kasa da dubu 50 da ake bukata wanda shi ne ya haifar da matsalolin cunkoson da ake fuskanta a irin wadannan gidaje.
Ya ce, akasarin wadanda aka fitar din ’yan kasa ne da suke daf da kare wa’adin zamansu a gidajen gyaran halin, kuma suna zaune cikin kunchi sakamakon gaza iya biyan tarar da aka yi musu tun da farko.
Ministan harkokin cikin gidan na tarayyar Najeriya ya sanar da cewa, adadin Naira miliyan dari biyar da tamanin da biyar ne daidaikun mutane ’yan kasuwa da kuma kungiyoyi masu zaman kansu suka tara domin dai samar da ’yanci ga fursunonin, inda ya ce, dukkan daurarren da tararsa ba ta wuce Naira miliyan daya ba an saka shi cikin wadanda suka amfana, kuma kowanne daga cikinsu ya samu wani tallafi na kudi da zai iya mayar da shi cikin al’ummarsa bayan samun horon koyon sana’o’i da suka yi yayin da suke a tsare.
“Ina amfani da wannan dama wajen kira ga al’umma da su karbi wadannan ’yan kasa hannu bibiyu, su kaucewa nuna kyama a gare su, domin gudun kada su sake komawa halayyarsu ta baya na karya dokar kasa, wanda hakan zai cutar da al’umma sosai.” (Garba Abdullahi Bagwai)