logo

HAUSA

Japan ta kawo karshen zango na 3 na aikin juye ruwan dagwalon nukiliya cikin teku

2023-11-20 16:08:52 CMG Hausa

A yau Litinin ne hukumar watsa labarai ta Japan ko NHK a takaice, ta bayyana cewa, an kawo karshen zango na 3 na ruwan dagwalon nukiliyar Fukushima Daiichi da kasar ke zubarwa cikin teku.

An dai fara gudanar da zangon na ukun ne tun daga ranar 2 ga watan Nuwamba, inda aka juye kimanin tan 7,800 na ruwan dagwalon a wannan karo. A jumlace, Japan din ta juye sama da tan 23,000 na wannan ruwa cikin teku tun fara aiki kawo yanzu. Majiyar ta ce Japan za ta fara gudanar da zango na 4 na aiki a farkon wata mai zuwa. (Saminu Alhassan)