logo

HAUSA

Kirkirar Aikin noman shinkafa bisa matukar kauna

2023-11-20 16:11:27 CMG Hausa


Ganin Zhu Shasha a karon farko, ba za ku yi tunanin wannan matashiya, kyakkyawa, mai kitson shuku, kwararriyar manomiya ce wadda ta nuna gwaninta a harkar noman shinkafa ba. A shekarar 2016, Zhu, mai shekaru 23, ta ajiye aikinta na malamar yara ta makarantar renon yara, ta fara aikin gona a kauyen Shuguang da ke yankin Xiaoshan na birnin Hangzhou, hedkwatar lardin Zhejiang a gabashin kasar Sin.

A cikin shekaru bakwai da suka gabata, ta zama “sabuwar manomiya,” wanda ta kware wajen sabon salon samar da amfanin gona, da kuma fasahohin noma na zamani. Yanzu, ita ce shugabar wata kungiyar hadin gwiwar noma, kuma ta karbi hayar gonaki fiye da hekta 133 a kauyen Shuguang.

Iyayen Zhu sun fara karbar hayar filin noma a kauyen Shuguang kusan shekaru 17 da suka gabata. Sun fara gajiya da aikin gona yayin da suka fara tsufa. Don haka, a shekarar 2016, Zhu Shasha ta karbi gonar da iyayenta suka yi haya, wanda ya mamaye kusan hekta 13.4, don sauke nauyin dake wuyan iyayenta. Tun daga wannan lokacin, ta karanci dabarun noman shinkafa, da yin amfani da hanyoyin kimiyya wajen kara yawan amfanin noman shinkafa, da kuma samar da sabbin nau'in shinkafa.

Zhu ta halarci ajujuwan horaswa da dama da suka hada da yadda ake sarrafa injunan noma da noman shinkafa. Ta yi amfani da ilimin da ta samu wajen habaka noman shinkafa, kuma ta karbi hayar karin filaye don shuka shinkafa. A shekarar 2019, yawan amfanin gona na shinkafa da ta samu ya kai kilogiram 13500 a kowace hekta, kuma gonarta ta kafa tarihi wajen samar da mafi yawan shinkafa a yankin Xiaoshan. A tsawon shekaru, ta lashe lambobin yabo da dama a matakin yanki saboda amfanin gonakinta masu yawan gaske.

Zhu Shasha ta ce, "duk da cewa na girma a kauye, ba kasafai nake yin aikin gona ba a da. Daga farko, yin aikin gona na mini wahala, lokacin da na koyi dabarun shuki daga wajen masana aikin gona. Sannu a hankali  na fara son aikin noma, kuma yanzu ina cike da sha'awar aikina."

A kowace safiya, Zhu tana rangadi a gonakinta, don lura da girman amfanin gona, da watsa taki, ko kuma fesa maganin kwari. Ta kan yi aiki har ta wuce lokaci. "A da, na fi son sanya siket da riguna masu kyau, yanzu, wando kawai nake sakawa wanda ya dace da aikin gona. Duk da haka, ina jin dadi idan na sami damar yin amfani da abin da na koya don magance matsalolin da suka shafi aikin gona da gyara injunan noma. Lallai kwalliya ta biya kudin sabulu", a cewar Zhu.

Ta shaida irin sauye-sauyen da aka samu a fannin noma na wurin da take zama. Tana mai cewa, “muna yin amfani da injuna sosai wajen aikin gona, muna da injunan kare amfanin gona marasa matuka, da na dashen shinkafa da sauran injunan ayyukan gona marasa matuka. Iyayena ba su taba tunanin cewa, wata rana injin zai taimaka wa manoma su yi aikin gona ba, a baya da hannayensu suke dasa shinkafa da watsa taki. Yanzu, muna sarrafa motoci marasa matuka don shuka iri da sanya taki." Zhu ta kara da cewa, “ina jin dadi idan na ga gonakin iyayena na kara kyau, mu ‘sabbin manoma’ ya kamata mu yi duk abin da za mu iya wajen bunkasa noman zamani, hakan zai taimaka wa kowane manomi a kasar nan da ya yi kyakkyawan fata ga harkar noma na nan gaba."

A gonakin Zhu Shasha, yin amfani da sabbin fasahohin noma da injunan noma sun samar da sakamako mai kyau. Idan aka kwatanta da shekaru 10 da suka gabata, yawan shinkafar da take samu a kowace hekta ya karu da kusan kilogiram 3000. Sauran manoman kauyen na nuna mata babban yabo, har ma suna kiranta “matashiya mai yawan noman hatsi”.  

Yin amfani da injuna wajen aikin noma ya taimaka wa manoma marasa adadi girbe shinkafar su. Shekaru shida da suka gabata, mai karancin fasahar girbi zai iya girbin kadada 1.33 ne kawai a kowace rana. Amma yanzu, ta hanyar amfani da injunan girbi da ke da fasahohin zamani, an girbe gona mai girman kusan hekta 3.3 a kowace rana. Zhu Shasha ta bayyana cewa, “cigaban da aka samu wajen girbi ya ninka fiye da ninki biyu. An kuma kara ingancin motar da nake aikin girbin da ita. An saka na'urar sanyaya iska a cikin motar, wanda ke sa direban gudanar da aikinsa cikin kwanciyar hankali."

Zhu tana samar da ayyuka daban-daban ga manoman kauyukan da ke kewaye, wadanda suka hada da noman hatsi da noman hatsi masu mai, da dashen shinkafa da injuna, da kare amfanin gona, da kuma amfani da tarakta wajen aikin noma. Bisa taimakon Zhu, mazauna kauyuka fiye da 20 sun kara yawan hatsin da suke girba a shekara da kilogiram 800 a kowace hekta.

Zhu Shasha ta gaya mun cewa, a nan gaba, za ta kara yin kokarin fadada hanyar sayar da shinkafa mai inganci, da kuma yin amfani da injunan noma masu kwakwalwa don inganta yadda ake noma.

Zhu tana da burika guda uku, wato noman shinkafa mai dadi, wadda ake watsa mata takin da ake samu daga halittu, da kafa tambarin hajojinta, da kuma kara girman filin gonaki da ta yi hayar zuwa hekta 200. A shekarar 2022, ta bar fili mai fadin hekta 6.67, inda ta yi kokarin shuka wani sabon nau'in shinkafa mai inganci. Ta samu girbi mai yawa, wanda  matsakaicin yawan amfanin gonar ya kai kilogiram 7500 a kowace hekta. Shinkafar tana da kamshi, kuma tana da laushi da taushi. Ta sayar da shinkafar ta hanyar WeChat, wani nau’in manhajar sadarwa da aika sakon kai tsaye ta kasar Sin. Yawancin kwastomominta sun maimaita sayen shinkafar mai inganci sau da yawa.

Zhu Shasha ta ce, “ina fata da yawan matasa, wadanda suka kware a fannin ilmi da fasahohin aikin gona, za su koma karkara, su fara sana’o’insu da suka shafi noma, da kuma bayar da gudummawa wajen farfado da karkarar kasar Sin.” (Kande Gao)