logo

HAUSA

Haduran hanya sun kashe mutane 1220 da raunata fiye da 11879 a jamhuriyar Nijar a shekarar 2022

2023-11-19 20:46:49 CMG Hausa

A ranar jiya 19 ga watan Nuwamban shekarar 2023, kasar Nijar tare da sauran kasashen Afrika sun yi bikin ranar yaki da haduran hanya, tare da jan hankalin shugabannin kasashe da gwamnatoci da ma kungiyoyin fararen hula kan wajabcin kawo karshen haduran motoci da na sauran ababen hawa da ke salwanta rayukan mutane.

Daga birnin Yamai abokin aikinmu, Mamane Ada ya turo ma da wannan rahoto.

 

Ita dai wannan ranar yaki da haduran hanya ta kasashen Afrika an sallace ta bisa taken “girmama ka’idojin hanya, wani matakin kishin kasa”, wacce kuma an gama ta tare da ranar duniya ta tunawa da mutanen da haduran hanya ya shafa. Ministan sufurin kasar Nijar, manjo kanal Salissou Mahaman Salissou a cikin wani jawabinsa zuwa ga ‘yan Nijar ya nuna cewa, taken wannan rana na tafiya daidai da lokaci. Inda ya bayyana cewa kasar Nijar za ta karbi bakuncin taruka karo na 12 na ranar Afrika ta yaki da haduran hanya daga ranar 25 zuwa ranar 26 ga watan Nuwamban shekarar 2023 a birnin Yamai.

A cewar ministan sufuri, Nijar na kasa ta 20 cikin kasashen Afrika 49 da ke fama da haduran hanya. Inda ya bayyana sakamakon haduran hanya na shekarar 2022 a Nijar inda aka samu haduran hanya 8561, da mutuwar mutane 1220, yayin da mutane 4321 suka ji rauni mai tsanani da 7558 suka samu rauni maras tsanani.

Haka kuma manjo kanal Salissou Mahaman Salissou, ya tabbatar da cewa ko wace shekara haduran hanya na karuwa a Nijar, inda ya ce tsakanin shekarar 2019 da shekarar 2022 an samu karuwa da kashi 10 cikin 100 na hadarin hanya.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.