Za a samar da hukumar lura da harkokin filaye da gine-ginen muhalli a Najeriya
2023-11-19 15:00:54 CMG Hausa
Ministan gidaje da bunkasar birane na tarayyar Najeriya Architect Ahmed Musa Dangiwa ya ce, shirye-shirye sun yi nisa wajen kirkiro da hukumar da za ta rinka kula da amfani da dokokin da suka shafi harkokin filaye da gine-ginen muhalli a Najeriya.
Ya tabbatar da hakan ne yayin babban taro karo na 12 na majalisar kula da gidaje da ci gaban birane ta kasa wanda aka gudanar a garin Kaduna, ya ce sabuwar hukumar idan aka samar da ita za ta jagoranci tsare-tsaren aiwatar da sabuwar dokar amfani da filaye wadda za ta maye gurbinta 1978 da ake amfani da ita yanzu.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Arc. Ahmed Dangiwa ya ce, gwamnatin shugaban Bola Ahmad Tinubu ta ci burin ganin cewa, ’yan Najeriya sun fita daga kalubalen mallakar gidaje, a kan haka nema aka bullo da sabbin tsare-tsare da manufofi managarta kuma masu dorewa da za su saukaka mallakar gidaje a birane da kuma manyan yankunan karkara ga kowanne dan kasa musamman masu karamin karfi.
Ministan ya ci gaba da cewa, sabuwar manufar samar da gidajen ta kasa, za ta samar da damarmaki ta fuskar ci gaban tattalin arziki da samar da aikin yi wanda zai fitar da miliyoyin ’yan Najeriya daga talauci, ha’ila yau sabon fasali a kan manufar filayen zai samar da kyakkyawan yanayi ga masu sha’awar saka jari a harkokin gine-ginen gidaje a kasar.
“A matsayina na ministan gidaje da raya birane a gaskiya dai ba na jin dadin yadda tsarin tafiyar da harkokin filaye a Najeriya ke tafiya, dalilan kuwa a bayyane suke, inda suka hada da rashin isassun tsarin bayanan kasa, daukar lokaci mai tsawo wajen aikin rajistar filaye lamarin da yake haifar da jinkirin mallakar takardu wanda hakan ke bayar da damar cin hanci da rashawa, haka kuma rashin daidaito da nuna gaskiya wajen aikin rajistar mallakar filaye yana kashe gwiwar masu saka jari, sannan kuma yana haifar da tawaya ga ci gaban tattalin arzikin kasa.” (Garba Abdullahi Bagwai)