logo

HAUSA

Harin Isra’ila kan wata makaranta a Gaza ya kashe Palasdinawa akalla 100

2023-11-19 16:15:24 CMG Hausa

 

Wata majiya daga jami’an lafiya na Palasdinu, ta ce harin bam na Isra’ila kan wata makaranta dake dauke da ‘yan gudun hijira a arewacin Gaza, ya yi sanadin kisan akalla Palasdinawa 100 tare da jikkata wasu gommai.

Majiyar ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an kwashe gawarwaki akalla 100 zuwa wani asibitin kasar Indonesia, bayan Isra’ila ta kai munanan hare-hare kan makarantar Al-Fakhoura dake sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia.

Ta kara da cewa, akwai yiwuwar samun karuwar adadin mamata sakamakon yadda ake ci gaba da gano gawarwaki daga cikin makarantar da kuma yadda mutane masu yawa ke cikin matsanancin yanayi.

Wata sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Masar ta fitar, ta bayyana a jiya cewa, harin da Isra’ila ta kai makarantar Al-Fakhoura, ya matukar keta hakkokin fararen hula a Gaza, haka kuma laifin yaki ne dake bukatar a yi bincike da hukunta wadanda ke da hannu.

Ma’aikatar ta kuma nanata kira ga kasa da kasa masu fada-a-ji da Kwamitin Sulhu na MDD, su shiga tsakani nan take domin kawo karshen mawuyacin halin da mutane ke ciki a zirin Gaza da dakatar da bude wuta ba tare da gindaya sharadi ba, da kuma samar da kariyar da ta kamata ga Palasdinawa fararen hula. (Fa’iza Mustapha)