logo

HAUSA

Shan isasshen ruwa na taimakawa na iya hana tsufa da kyautata lafiya

2023-11-18 23:09:09 CMG Hausa

 

Wani nazarin da aka gudanar a kasar Amurka ya nuna cewa, in an kwatanta wadanda ba sa shan ruwa isasshe, za a ga cewa, baligan da suka shan ruwa isasshe sun kara samun lafiyar jiki, kuma barazanar da suke fuskanta wajen kamuwa da cututtukan da ke addabar mutane cikin dogon lokaci ta ragu, kana sun fi samun tsawon rai.

Masu nazari daga kwalejin nazarin lafiya karkashin shugabancin ma’aikatar lafiya da ba da hidimomin al’umma ta kasar Amurka, sun tantance bayanan lafiyar baligai dubu 11 da dari 2 da 55 cikin shekaru 30. Inda suka yi bincike kan yadda suka je ganin likita sau 5 cikin wadannan shekaru 30, da kuma yin nazari kan alakar da ke tsakanin yawan sinadarin serum sodium da lafiyar mutanen. Sai kuma sau biyu bayan da shekarun wadannan mutane suka wuce 50 a duniya, da kuma karo na karshe yayin da shekarunsu suka wuce 70 amma ba su kai 90 a duniya ba.

Idan mutane sun sha ruwa isasshe, yawan sinadarin serum sodium zai ragu, idan kuma ba su sha isasshen ruwa ba, yawan wannan sinadari zai karu.

Sakamakon nazarin ya nuna cewa, wadanda suke da yawan sinadarin serum sodium a cikin jikinsu, ga alama sun fi tsufa, gwargwadon wadanda ba su da yawan wannan sinadari a cikin jikinsu. Ma iya cewa, sun fi saukin gamuwa da matsaloli a tsarin jijiyoyin zuciya, kuma karfin huhunsu kan ragu. Ban da haka kuma, cikin wadanda suke samun daidaiton yawan serum sodium a cikin jikinsu, karuwa yawan serum sodium, ya kan kara musu barazanar tsayawar bugun zuciya, da kumwa da matsalar shanyewar sassan jiki, ciwon zuciya, ciwon jijiyoyin zuciya, ciwon huhu da ke addabarsu cikin dogon lokaci, ciwon sukari da lalurar karancin basira.

Dangane da lamarin, madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing, ta yi mana karin bayani da cewa, sakamakon nazarin ya tunatar mana da cewa, shan ruwa isasshe yana iya hana tsufa da kara zama cikin koshin lafiya.

Ta kara da cewa, watakila shan ruwa isasshe yana amfana wa lafiyar wadanda suke da sinadarin serum sodium mai yawa a cikin jikinsu. Yawancin mata na bukatar shan ruwan da ya kai lita 1.5 zuwa lita 2 a ko wace rana, ko ruwan lemu ko cin ‘ya’yan itatuwa masu dauke da ruwa. Maza kuma suna bukatar shan ruwan da ya kai lita 2 zuwa lita 3 a ko wace rana. Duk da haka, wadanda ba su da koshin lafiya ya fi kyau su saurari shawarar likita game da adadin ruwan da ya kamata su rika sha a ko wace rana.

Har ila yau, masu nazarin na Amurka sun yi bayani da cewa, nazarinsu bai tabbatar da cewa, shan ruwa isasshe, dalili ne da zai iya hana tsufa ba. Akwai bukatar ci gaba da nazari. Amma sakamakon nazarinsu ya ba da shawara kan yadda mutane za su kula da lafiyarsu game da muhimmancin shan ruwa ga lafiyarsu. (Tasallah Yuan)