logo

HAUSA

Xi ya gabatar da wani shiri: kirkirar "shekaru 30 masu fa’ida" nan gaba na ci gaban yankin Asiya da Pasific

2023-11-18 16:04:17 CMG Hausa

An gudanar da kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar hadin gwiwar raya tattalin arzikin yankin Asiya da Pasifik ko APEC a takaice a San Francisco na Amurka a jiya Jumma’a bisa agogon Amurka.

A cikin shekaru 30 da suka gabata, “abubuwan ban al’ajabi” da mambobi 21 na kungiyar APEC suka kafa tare sun jawo hankalin kasa da kasa. A nan gaba kuma, yaya yankin Asiya da Pasifik zai cimma "shekaru 30 na ci gaba"? Shugaban Sin Xi Jinping ya ba da amsa a cikin jawabinsa, kuma abu mafi muhimmanci a ciki shi ne tsayawa tsayin daka kan bude kofa da hadin gwiwa da kuma samun ci gaba tare.

Ya kuma gabatar da shawarwari guda 4 a cikin jawabinsa, wato tsayawa tsayin daka kan samun bunkasuwa ta hanyar kirkire-kirkire, da nacewa kan bude kofa ga kasashen waje, da tsayawa tsayin daka kan samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da kuma tsayawa tsayin daka kan kawo alheri ga dukkan al’ummun kasashen duniya. Kuma abu mafi muhimmanci a cikinsu shi ne tsayawa tsayin daka kan ra’ayin bude kofa ga kasashen waje da yin hadin gwiwa da kuma samun ci gaba tare. Wannan ra’ayi shi ne tushen shirin Xi Jinping, kuma shi ne ruhin tarihin ci gaban yankin Asiya da Pacific a cikin shekaru 30 da suka gabata.

"Bude kofa yana haifar da wadata, yayin da rufe kofa ke haifar da koma baya." Xi Jinping ya sha bayyana cewa, wannan ita ce muhimmiyar kwarewar da ta taimakawa Sin da ma duniya wajen samun ci gaba. Tarihin wadatar yankin Asiya da Pacific ya kuma shaida cewa, rashin hadin kai babban hadari ne.(Safiyah Ma)