logo

HAUSA

An kaddamar da sabbin sharudan yarjejeniyar cigaba ga yankunan da ake hakar ma`adanai a Najeriya

2023-11-18 13:25:45 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta hannun ma`aikatar ma`adanai tare da hadin gwiwa da cibiyar jagoranci da tsare-tsaren cigaba ta Afirka sun kaddamar da sabon kundin yarjejeniyar kyautata rayuwar al`ummomin dake zaune a yankunan da ake hakar ma`adanai.

A lokacin da yake jagorantar kaddamar da daftarin yarjejeniyar a birnin Abuja, ministan cigaban harkokin ma`adanai na tarayyyar Najeriya Dr. Dele Alake, ya ce sabbin sharudodin dake kunshe a cikin yarjejeniyar zai baiwa al`ummmonin damar cin gajiya daga ayyukan kamfanonin hakar ma`adanai ba tare da kace-nace ba, sannan su kuma kamfanonin su rinka biyan hakkokin gwamnati yadda ya kamata.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Dr. Dele Alake yace babban makasudin sabunta wannan yarjeejniya shine tabbatar da ganin gwamnati tana amfana sosai daga dinbun albarkatun kasar da ake dasu jibge a sassa daban daban, kasancewar yanzu irin wadannan albarkatu sune suka maye gurbin man fetur a duniya.

Ministan ya kara dacewa a halin da ake ciki duniya tana sauyawa daga makamashin dake gurbata muhalli zuwa ma`adanan da suke samar da makamashi mai tsafta.

Ya nanata cewa babu wani kamfanin hakar ma`adanai a Najeriya da baya amfana ta fuskar riba, a saboda haka dole ne kuma irin wadanann kamfanoni su lura da ingancin muhallin al`ummomi, ha` ila yau ya ja kunne irin wadannan kamfanoni cewa lokacin bujirewa biyan hakokin gwamnati da suka jibinci haraji da diya ya wuce.

“ A matsayin mu na masu sanya ido zamu tabbatar da ganin ana aiki da dukkan sharuddan dake cikin wannan sabuwar yarjejeniya, sannan su kuma al`umomin da suke zaune a yankunan da ake hakar ma`adanan, wajibi ne su samar da yanayi mai kyau mara cutarwa wajen samun nasarar ayyukan kamfanonin hakar ma`adanai a yankunan su.”

Ministan yace muddin babu zaman lafiya, to kuwa babu wanda zai amfana da wani abu.(Garba Abdullahi Bagwai)