logo

HAUSA

Shugaban kasar Liberia ya amince da shan kaye a babban zaben kasar

2023-11-18 15:19:31 CMG Hausa

Shugaban kasar Liberia George Weah, ya amince da shan kaye a zagaye na biyu na babban zaben kasar. Wanda abokin takararsa Joseph Boakai ya lashe, a wani jawabin da ya gabatar ta gidan rediyo na kasar Liberia, jiya Juma’a.

Sakamakon zaben da aka gabatar ya nuna cewa, an riga an kidaya kashi 99.5% na kuri’un da aka kada a zaben na ranar Talata, inda Boakai ya samu kaso 50.89 na kuri’un, ta yadda ya doke shugaba mai ci da ya samu kaso 49.11.

Weah ya amince da shan kaye, kana ya taya Boakai murnar nasarar da ya samu. Yana mai cewa Laberiya ce ta yi nasara, kuma lokaci ya yi da za a fifita muradun kasa fiye da bukatun mutum. (Bello Wang)