logo

HAUSA

Gimbiya Sirindhorn ta Thailand:shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ta inganta hadin gwiwar al’ummun kasa da kasa

2023-11-18 13:08:11 CMG Hausa

A kwanakin baya ne, gimbiya Maha Chakri Sirindhorn ta kasar Thailand, ta yi tsokaci kan muhimmancin shawarar "Ziri daya da Hanya Daya" da kasar Sin ta gabatar, yayin wata hira da wakiliyar gidan telabijin na CGTN a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Ta bayyana cewa, layin jiragen kasa tsakanin kasashen Sin da Laos da Thailand da aka gina karkashin shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” yana da muhimmanci matuka, domin gina layin dogon zai inganta ci gaban tattalin arziki. Ta hanyar hada layin dogon, mu'amalar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen Thailand da Sin za ta ci gaba da karuwa, kuma jama'ar Thailand da ta Sin za su iya yin hadin gwiwa wajen zuba jari a wasu ayyuka. 

Ta kara da cewa, a halin yazu, layin jiragen kasa tsakanin Sin da Laos ya hada wurare daban daban na kasashen 2, kuma ya hada Turai dake yammacin duniya. Kana a nan gaba, za a hada layin jiragen kasa na Sin da Thailand da layukan dogo da aka gina a baya.

Gimbiya Sirindhorn ta yi imani cewa, ba ma kawai layin jiragen kasa na Sin-Laos-Thailand zai inganta ci gaban tattalin arzikin kasashen ba, har ma zai taimakawa raya tattalin arzikin sauran kasashe. Shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ta ba al’ummun Thailand da Sin da na kasashe daban daban damar yin hadin gwiwa tare. Ta wannan shawara, Sinawa da dama sun zo Thailand don zuba jari, a sa’i daya kuma mutanen Thailand masu yawa sun je Sin don zuba jari. Ban da zuba jari a fannin cinikayya, shawarar ta taimaki jama’a wajen samun saukin tafiye-tafiye da yawon shakatawa. Saboda haka wannan shawara ce mai kyau, wadda ke da ma’ana sosai.(Safiyah Ma)