logo

HAUSA

Wace hanya yankin Asiya da Pasifik zai bi don sake kirkiro al’ajabi a shekaru 30 masu zuwa?

2023-11-18 21:35:21 CMG Hausa

A bana ne ake cika shekaru 30 da kaddamar da kwarya-kwaryan taron shugabannin kungiyar APEC karo na farko, wato kungiyar hadin-gwiwar tattalin arzikin yankin Asiya da tekun Pasifik. Tambaya a nan ita ce, yaya yankin Asiya da na tekun Pasifik zai kasance daga nan har zuwa tsakiyar karnin da muke ciki? Kuma wane kokari ya kamata a yi domin kara samar da ci gaba a wannan yanki a cikin shekaru 30 masu kamawa?

A ranar 17 ga watan Nuwamban nan bisa agogon wurin, a wajen kwarya-kwaryan taron shugabannin APEC karo na 30 da aka yi a birnin San Francisco na kasar Amurka, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a samar da ci gaba mai inganci a yankin Asiya da na tekun Pasifik, da yin alkawarin cewa, kasarsa za ta samar da sabbin damammaki ga sauran kasashe don su zamanantar da kansu, bisa zamanantarwa irin ta kasar Sin.

Samar da ci gaba mai inganci, muhimmin abu ne a harkokin raya kasar Sin. Tun daga samar da ci gaba mai inganci ga kasar Sin, har zuwa samar da ci gaba mai inganci ga yankin Asiya da na tekun Pasifik, wace irin alaka hakan ya kunsa? Darekan cibiyar nazarin APEC ta jami’ar Nankai ta kasar Sin, Liu Chenyang ya bayyana cewa, kasar Sin ta kara samun fahimta kan ainihin ma’anar “samar da ci gaba mai inganci”, wadda ke kunshe da fannonin yin kirkire-kirkire, da kiyaye muhallin halittu, da bude kofa ga kasashen waje, daidai da kokarin da ta yi na habaka tattalin arziki, kana, tana fatan raba dabarunta zuwa ga yankin Asiya da na tekun Pasifik, ta yadda membobin kungiyar APEC za su kara bunkasa.

A shekaru 30 da ke tafe, kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa samar da ci gaba mai inganci ga yankin Asiya da na tekun Pasifik, da tabbatar da aiwatar da ajandar Putrajaya nan da shekara ta 2040, domin kara sanya kuzari ga zamanantar da duk fadin duniya. (Murtala Zhang)