Xi Jinping ya gabatar da wani shiri: kirkirar "shekaru 30 masu fa’ida" nan gaba na ci gaban yankin Asiya da Pasific
2023-11-18 21:06:27 CMG Hausa
An kammala kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar hadin gwiwar raya tattalin arzikin yankin Asiya da Pasifik, ko APEC a takaice, a San Francisco na Amurka, jiya Jumma’a. A cikin jawabinsa a yayin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani shiri: kirkirar "shekaru 30 masu fa’ida" nan gaba na ci gaban yankin Asiya da Pasific.