logo

HAUSA

‘Yan Nijar na gida da waje sun bayyana fatan wata dangantaka ta moriyar juna tare da kasar Sin

2023-11-18 16:06:33 CMG Hausa

Tun bayan zuwan sabbin shugabannin soja a kasar Nijar dalilin juyin mulkin ranar 26 ga watan julin shekarar 2023, da kuma matakin kungiyar CEDEAO na sanyawa kasar takunkumin tattalin arziki dana kudi yau da kusan watanni hudu, a yanzu al’amura na fara daidaita tare da taimakon wasu taimakon kasashe da suka ci gaba da taimakawa Nijar bisa hanyar gina kanta, dalilin kenan abokin aikinmu daga birnin Yamai ya hiranta ta da wasu ‘yan Nijar kan makomar kasar musammun ma tare da wasu kasashe kamar kasar Sin. Ga abin da suke cewa :

Sunana Salisu Labo Waziri, dan canji a Maradi, jamhuriyyar Nijar. To wannan abin farin ciki ne gare mu ‘yan Nijar, muna fatan Allah watabaraka yasa matasanmu za su samu ayyukan yi, arziki ya shigo cikin kasa. Duk matashi ya samu aikin yi, idan Allah ya yarda to ba za’a maganar wani ta’addanci cikin kasa ba. Allah ya kara daukaka kasar Nijar, Allah ya kara ba mu zaman lafiya.

Sunana Adamu Arzika Maman Musa, dan Nijar mazaunin Najeriya, wanda ni ke a garin Bauci State, Azare katabum local gouvment, allahamdu lillahi muna ganin abubuwa a Nijar, insha Allahu duk da cewa, an sanya mana wasu takunkumai, idan Allah ya yarda wannan abu zai bunkasa, kuma nuna kyautata zaton mu da muke ketare ‘yan Nijar, muna sa ran za mu dawo gida, insha Allahu, sannan kuma game da dangantaka tsakanin Nijar da kasar China, wannan dangantaka ta jima ba tun yau ba, ba ma a fannin hidimar man fetur ba ma, har a fannin lafiya da sauran abubuwa, kasar China tana taimakawa kasar Nijar sosai da sosai, ba tun yau ba.

Assalamu alaikum waramtullahi wabarakatuhu, to Allahamdu lillahi, sai mu yi godiya wajen Allah saboda China kasa ce, wanda duk inda ta shiga haraka ce, ta arziki take yi.

Assalamu alaikum waramatullahi wabarakatuhu, sunana Sale Leko wanda ake kira Ashata mai alewa, dan Nijar, mazaunin Cote d’Ivoire, to Allahamdu lillahi, allahamdu lillahi na ji dadi da kasata ta samu ci gaba haka, kuma sojoji masu mulki, duk wani kucece kucece da ake da dumumuwa su yi banza da wannan abin su ci gaba da aikin da suka sa gaba.

(Mamane Ada)