logo

HAUSA

An kammala kwarya-kwaryar taron shugabannin APEC karo na 30 a San Francisco

2023-11-18 14:41:45 CMG Hausa

An kammala kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar hadin gwiwar raya tattalin arzikin yankin Asiya da Pasifik, ko APEC a takaice, a San Francisco na Amurka, jiya Jumma’a.

Taron ya fitar da "Sanarwar Shugabannin APEC na San Francisco na shekarar 2023", inda aka jaddada cewa, dole ne kungiyar APEC ta yi amfani da ci gaban fasahohi da tattalin arziki, don ci gaba da tabbatar da yanayi mai armashi da yankin ke da shi, da samun karuwar tattalin arziki, da tinkarar dukkan kalubaloli masu alaka da  muhalli, misali sauyin yanayi, da sai sauransu.

Taken taron na wannan karo shi ne “Samar da makoma mai karfi da dorewa ga dukkan al’umma”.(Safiyah Ma)