logo

HAUSA

ECOWAS Ta kafa cibiyar samar da bayanai don inganta tsarin samar da wutar lantarki

2023-11-18 10:43:03 CMG Hausa

A jiya ne, aka kaddamar da cibiyar samar da bayanai da daidaita tsarin samar da wutar lantarki (WAPP) ta kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) a birnin Abomey Calavi da ke kudancin kasar Benin.

Manufar cibiyar ita ce, ingantawa da bunkasa samar da wutar lantarki da hanyoyin raba shi, da kuma daidaita tsarin musayar wutar lantarki tsakanin kasashe mambobin kungiyar ECOWAS.

Haka kuma, cibiyar wani dandali ne na daidaita ayyukan WAPP, wanda zai ba da damar shigar da hanyoyin samar da wutar lantarki na kasa cikin hadaddiyar kasuwar samar da wutar lantarki ta yanki, don tabbatar da ganin an samar da tsayayyen farashi mai inganci ga jama’ar kasashen kungiyar ECOWAS a cikin matsakaici da kuma dogon lokaci.

Mataimakin shugaban hukumar ECOWAS Damtien L. Tchintchibidja, ya bayyana cewa, tsarin zai ba da damar saye da sayar da wutar lantarkin, tun daga rubu’i na farko na shekarar 2024, ba tare da la’akari da wurin da yankin yake ba. (Ibrahim)