logo

HAUSA

An nada sabon wakilin MDD a Sudan

2023-11-18 10:04:28 CMG Hausa

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya nada Ramtane Lamamra a matsayin manzon musamman na babban sakataren majalisar mai kula da Sudan, biyo bayan bukatar kasar, na kawo karshe aikin tawagar majalaisar mai kula da harkokin siyasa (UNITAMS) a kasar da yaki ya daidaita.

Mai magana da yawun magatakardan majalisar Stephane Dujarric, ya bayana cewa, MDD za ta ci gaba da hada kai da mahukuntan Sudan, bayan tabbatar da samun wata wasikar da jami'an kasar suka aika mata, wadda a cikinta aka bayyana matakin da gwamnatin kasar ta dauka na kawo karshen aikin tawagar UNITAMS a kasar.

Kakakin ya ce, majalisar za ta ci gaba da yin aiki kafada da kafada da dukkan masu ruwa da tsaki, ciki har da hukumomin Sudan, da mambobin kwamitin sulhu, domin fayyace matakai na gaba.

Yana mai cewa, kwamitin sulhu ne ya baiwa sakatariyar wa'adin gudanar da ayyukan samar da zaman lafiya, da na siyasa da yadda tawagogin wanzar da zaman lafiya za su gudanar da ayyukansu. (Ibrahim)