logo

HAUSA

Malamai da dalibai 'yan Tanzaniya 132 sun lashe lambar yabo ta jakadan kasar Sin saboda kwazo a harshen Sinanci

2023-11-17 10:17:30 CMG Hausa

A jiya ne, aka ayyana a kalla malamai da dalibai 'yan kasar Tanzania 132, a matsayin wadanda suka lashe lambar yabo ta jakadan kasar Sin karo na 6, saboda gudummawa ta musamman da suka bayar a koyar da harshen Sinanci, ko yin fice a fannin koyon Sinanci a shekarar 2023.

Wadanda suka yi nasarar da aka ba su kyautuka daban-daban a yayin wani bikin da aka gudanar a ofishin jakadancin kasar Sin dake Dar es Salaam, sun hada da dalibai 125 da kuma malamai 7 da suka fito daga makarantun sakandare 18 da jami'o'i 5 na kasar Tanzania.

A jawabinsa yayin bikin, ministan ilimi, kimiyya da fasaha na kasar Adolf Mkenda, ya bayyana cewa, koyon harshen Sinanci ba kawai ya amfanar da dalibin ci gaban kansa na dogon lokaci ba, har ma zai ba da gudummawa ga zumunci da hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Tanzaniya nan gaba. (Ibrahim)