logo

HAUSA

Xi ya gana da firaministan Japan da sultan na Brunei

2023-11-17 10:55:05 CGTN HAUSA

 

Da yammacin jiya bisa agogon wurin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Japan Fumio Kishida da sultan wato shugaban kasar Brunei Haji Hassanal Bolkiah a San Francisco na kasar Amurka.

Yayin ganawarsa da firaministan Japan, shugaba Xi ya bayyana cewa, a bana ake cika shekaru 45 da Sin da Japan suka kulla yarjejeniyar zaman lafiya da sada zumunta tsakaninsu. Yarjejeniyar ta kafa cikakken alkiblar zaman lafiya,da abokantaka, da hadin gwiwa tsakanin Sin da Japan bisa doka, da jaddada adawa da ra'ayin nuna babakere, wadda ta aza wani muhimmin tubali ga huldar kasashen biyu. Zama tare cikin lumana, da abokantaka mai dorewa, da hadin gwiwar moriyar juna, da samun ci gaba tare, sun dace da muhimman muradun jama'ar Sin da Japan. Kamata ya yi bangarorin biyu su yi amfani da zarafi mai kyau da ake samu don mai da hankali kan muradun dake jawo hankalinsu, da daidaita bambancin ra’ayi yadda ya kamata, da kiyaye ka’idojin dake kunshe cikin takardun siyasa guda hudu a tsakaninsu, da tabbatar da matsaya kan huldar kawowa juna moriya bisa manyan tsare-tsare, da dukufa kan kafa huldar kasashen biyu dake dacewa da halin da ake ciki a sabon zamani.

Ban da wannan kuma, a yayin ganawarsa da shugaban kasar Brunei Haji Hassanal Bolkiah, shugaba Xi Jinping ya ce, a bana ake cika shekaru 5 da kulla dangantakar abota ta hadin kai bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Brunei. Kasar Sin tana son hadin gwiwa tare da Brunei, don ci gaba da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da ci gaba da inganta hadin gwiwa mai inganci, wajen gina shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", da samar da karin moriya ga jama'ar kasashen biyu. (Amina Xu)