logo

HAUSA

Yadda za a sake farawa daga birnin San Francisco

2023-11-17 22:21:21 CMG Hausa

Kafin tafiyarsa, Amurkawa sun yi bankwana cikin bege, suna fatan wasu sabbin dabbobin Panda za su je kasar a nan gaba. Da yammacin ranar Laraba, a lokacin da ya halarci liyarfar maraba da kungiyoyin abokai na Amurka suka shirya a birnin San Francisco, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana aniyar ci gaba da hadin gwiwar kare dabbobin Panda da Amurka, domin karfafa abota tsakanin al’ummomin kasashen biyu.

Dabbar Panda ta shaida huldar abota tsakanin Sinawa da Amurkawa. Hakika, dangantakar kasashen biyu, sakamako ne na dangantakar al’ummominsu. Tun daga lokacin baya zuwa yanzu, musayar da bata gwamnati ba, ta kasance karfin dake ingiza ci gaban dangantakar. A wannan karo, shugabannin Sin da Amurka sun cimma matsaya cewa, kasashen biyu za su kaddamar da karin matakai na inganta musaya tsakanin jami’ansu da inganta musayar al’adu tsakanin al’umominsu.

San Francisco ya shaida tarihin musaya tsakanin al’ummomin Sin da Amurka, kuma a yanzu, ya kara shaida sabon ci gaban musaya tsakanin bangarorin biyu. Ba tare da la’akari da sauyin da ka iya zuwa ba, burikan musaya da hadin gwiwa tsaknain al’ummomin Sin da Amurka ba zai sauya ba. Da muka sake farawa a San Francisco, karin mutane ne ke buga ganga tare da ihun raya dangantakar Sin da Amurka. Wannan wani tubali ne mai kwari na ingantawa tare da raya huldar bangarorin biyu. (Fa’iza Mustapha)