logo

HAUSA

Masana: Wajibi ne Amerika ta samu sulhu da China muddin tana son dorewar tagomashinta a kasashen duniya

2023-11-17 13:14:27 CMG Hausa

Masana a Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan yunkurin Amurka na gyara hulda diplomasiyyarta da kasar Sin, a daidai lokacin da tauraron kasar Sin ke ci gaba da haskawa a kasashe masu tasowa musamman nahiyar Afrika.

Da yake zantawa da wakilinmu dake Najeriya ta wayar tarho, Dr Abdulsalam Muhammad Kane, malami a jami’ar ilimi ta Sa’adatu Rimi dake jihar Kano a arewacin Najeriya, ya yi bayani kamar haka: