logo

HAUSA

Xi ya halarci kwaya-kwaryan taron shugabannin mambobin APEC

2023-11-17 09:39:15 CGTN HAUSA

 

Da tsakar ranar jiya agogon wurin ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci kwarya-kwaryar taron tattaunawa da kuma liyafar cin abincin rana tsakanin shugabannin mambobin kungiyar APEC da baki da suka karbi bakuncinsu a San Francisco na kasar Amurka. A yayin taron, Xi Jinping ya nuna cewa, a ’yan shekarun baya-bayan nan, kungiyar APEC ta kara karfin tabbatar da manufofin Putrajaya nan da shekaru 2040, da kuma tabbatar da manufofin Bangkok na samun ci gaban tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, ta yadda za a taka rawa a bangaren samun bunkasuwa a duniya ba tare da gurbata muhalli ba. A bisa halin da ake ciki yanzu, kamata ya yi, kasashe daban-daban su kai ga cimma matsaya daya da daukar mataki tare, don ba da gudunmawarsu a wannan fanni. Kan haka Xi Jinping ya ba da shawarwari guda uku:

Na farko, gaggauta tabbatar da ajandar samun ci gaba mai dorewa ta MDD nan da shekarar 2030. Kana Sin kuma ta gabatar da shawararin samun bunkasuwar duniya, wanda zai taka rawa wajen karawa kasashen duniya kwarin gwiwar hada kai don tinkarar gibin da ake samu ta fuskar ci gaban tattalin arziki.

Na biyu, a fito da wata sabuwar hanyar samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, ta yadda za a kafa wani yanayi mai adalci tsakanin bunkasuwar tattalin arziki da kiyaye muhalli.

Na uku, hadin kan kasashen duniya wajen tinkarar sauyin yanayi. Kiyaye yarjejeniyar MDD kan sauyin yanayi a matsayin babbar hanyar tafiyar da harkoki masu alaka da yanayin duniya. Da magance matsalolin da ke damun kasashe masu tasowa ta fuskar kudade, inganta kwarewa da musayar fasahohi, ta yadda za a tabbatar da yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayi na MDD da ta Paris.

Ban da wannan kuma, Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin tana kokarin tabbatar da shawarar “ziri daya da hanya daya” a bangare kiyaye muhalli, za kuma ta ci gaba da gina manyan ababen more rayuwa ba tare da gurbata muhalli ba, da samar da tsabtaccen makamashi da amfani da shi a fannin zirga-zirga. Sin na fatan hada kai da bangarori daban-daban don kara ba da gudunmawa wajen gina kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya na samun bunkasuwa tare, da samar da yanayi mai kyau a duniya.

Shugaban kasar Amurka Joe Biden ne ya jagoranci wannan taro mai taken “Samun bunkasuwa mai dorewa da lura da sauyin yanayi da zamanintar da makamashi.”

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi shi ma ya halarci wannan taro.(Amina Xu)