logo

HAUSA

Wannan kyauta ce ta musamman daga daliban makarantar sakandaren Amurka

2023-11-17 15:15:38 CMG Hausa

A jiya ne, babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da kungiyoyi irinsu kungiyar musayar daliban kasashen Sin da Amurka, suka shirya taron "musayar al'adu da sada zumunta tsakanin Sin da Amurka" a birnin San Francisco na kasar Amurka. Inda wasu daliban wata makarantar sakandare na kasar Amurka sun gabatar da wani zanen da suka tsara a matsayin kyauta ga shugaban kasar Sin Xi Jinping da mai dakinsa Peng Liyuan. Kana Shen Haixiong, shugaban CMG, ya karbi kyautar a madadinsu. (Bello Wang)